Labarai

‘Yan Najeriya na Allah-wadai da karbar tuban Bello Turji

 

Bello Turji ya yi ficewa wajen garkuwa da mutane da kuma aikata kisa

Al’ummar Najeriya na ci gaba da Allah-wadai tun bayan fitowar wasu bayanai kan fitaccen ɗan bindigar nan Bello Turji Kachalla da ake cewa ya rungumi sulhu bayan tabbatar da tubansa.

A ranar Lahadi ne gwamanatin Zamfara ta fitar da wata sanarwa da ke cewa fitaccen ɗan bindigar ya tuba, kuma ya rungumi zaman lafiya bayan ya shafe shekaru ya na satar mutane da kashe na kashewa.

Sai dai wannan labari ya zo wa galibin ‘yan kasar da ke ɗiga ayar tambaya da mamaki, inda galibin mutane har a shafukan sada zumunta ke tafka muhawara da nuna shakku kan tuban Bello Turji.

Mataimakin gwamanan Jihar ta Zamfara ne ya gabatar da sanarwar game da mutumin da yawancin mutane a arewacin Najeriya ke kira ‘Sarkin ‘yan Ta’adda.

An dai shafe shekaru jami’an ‘yan sanda na nemansa ruwa-a-jallo domin laifukan ta’addancin da ake tuhumarsa da aikatawa a jihohin Zamfara da kuma Sokoto da Katsina masu makwabtaka.

Wannan ne ya sa awancin mazauna jihar ta Zamfara ke bayyana shakku bayan da suka sami labarin tuban Bello Turji.

Sun riƙa bayyana rashin amincewarsu da wannan labarin inda wasunsu ke cewa ɗan bindigar ba abin da za a amince da shi ne ba.

Ra’ayin ma’abota shafukan sada zumunta

An rinka tafka muhawara kan karbar tuban Bello Turji a shafukan sada zumunta irinsu Facebook da Tuwita.

Ga abin da wasunsu ke cewa.

@kabirMukhtar91 ya ce, “Na kasa fahimtar dalilin da ya sa gwamnatin Jihar Zamfara ta ke damun mu da batun yaronta Bello Turji a duk lokacin da jami’an tsaro suka ɗauki matakin kawo ƙarshen ‘yan bindiga a jihar, sai kawai ya ce ya rungumi zaman lafiya ko ya tuba.”

@ChNdozieNGR ya ce, “Mun sha jin irin waɗannan labaran a da. ‘Yan bindiga ba sa tuba. Kulla yarjejeniya da ‘yan bindiga bai taba aiki ba, kuma ba zai taba aiki ba.”

@Abou_Sidra_ ya ce “Akwai tambayoyin da ke bukatar gwamnatin Zamfara ta amsa su kan yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da shugaban ‘yan bindiga bello Turji. Wa ya ba shi lasisi da makaman da zai kashe sauran ‘yan bindiga. Wa ke biyan kuɗin diyya?”

@rotimiinlagos ya ce, “Tuba? Wace irin tuba? Ina batun adalci ga wadanda ya kashe, da bala’in da ya janyo? ya biya diya ne? Akwai kudaden da ya dawo da su? Tuba?! Anya!!!

@AdamsUsaubu ya ce, “Karya ce. Zai koma aikinsa na dan bindiga.” @zaheedayoola kuwa cewa yayi, “Kar ku yarda da makaryacin. Ku aika da shi ga mahaliccinsa domin ya yi masa hukunci kawai.”

Wasu abubuwan da su ka kamata ku sa ni game da Bello Turji

Bello Turji Kachalla wanda aka fi sani da Turji, wani ɗan bindiga ne da ya yi kaurin suna a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Ɗan bindigan wanda aka haifa a shekarar 1994, ya addabi jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Neja.

Shi ne ya jagoranci harin da wani gungun ‘yan bindiga suka kai kan wasu al’umomi a Jihar Zamfara wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 200, ciki har da mata da kananan yara.

Dr. Murtala Ahmed Rufa’i malami ne a tsangayar tarihi ta Jami’ar Usmanu Danfdio da ke Sokoto, kuma shi ne ya wallafa littafi mai suna ‘Ni dan bindiga ne’ ya bai wa BBC wasu bayanai a game da abubuwan da ya sani game da Bello Turji.

”An haife shi a karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara. Sai dai a lokacin da aka hafe shi Zamfara da Sokoto na tare cikin jiha daya ce, wato tsohuwar Jihar Sokoto.

“A Shikafi aka haife shi, kuma tun yana karami mahaifinsa ke tafiya da shi kasuwannin sayar da dabbobi daga Shinkafin, kamar dai yadda kowane dan Fulani ke yi wa ‘ya’yansa,” inji Dakta Murtala.

Malamin jami’ar ya kara da cewa a halin yanzu, shekarun Belo na haihuwa tsakanin 27 zuwa 35 ne.

“Mahaifinsa Usman mutumin kirki ne wanda ke zaman lafiya da makwabtansa a yankin Shinkafi.”

Amma akwai rahotannin da ke cewa dukkan ‘yan uwan Bello Turji sun juya masa baya saboda ba sa son abubuwan da yake yi.

Dakta Murtala ya ce saboda ta’asar da dansa ke aikatawa ne mahaifin Bello ya koma garin Kura da ke Jihar kano, kuma daga can ya koma Jihar jigawa.

“Dukkan ‘ya uwansa ba sa goyon bayan shi, kuma ma ba sa karbar dukkan kayan da yake ba su saboda suna kallon abin a matsayin babban laifi,” inji Dakta Murtala.

Zurfin ilimi

Bello Turji Dakta Murtala ya ce Bello Turji ya sami ilimin addinin Islama daidai gwargwado, amma a ɓangaren ilimin boko makarantar firamare kawai ya halarta.

“Yana da ilimin addinin Musulunci amma bai yi zurfi ba kamar yadda wasu ke tsammani. Sai dai firamare kawai ya gama a ɓangaren ilimin boko.”

Rayuwar Bello Turji

Dakta Murtala ya ce cikin ‘yan shekarun da suka gabata ne Bello ya fara shiga wannan matsalar, domin lokacin da rashin zaman lafiya ya ɓarke a Zamfara, Bello bai gama girma ba.

‘Ba a dade ba da ya rungumi rayuwar ɗan bindiga’

Malamin jami’ar ya kuma ce Bello ya fara da satar shanu ne kafin daga baya ya koma satar mutane da ayyukan ‘yan bindiga baya da ya rika.

 

The post ‘Yan Najeriya na Allah-wadai da karbar tuban Bello Turji appeared first on VOICE OF AREWA.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news