Ciwon Lafiya

‘Yan Najeriya sun yi wa Korona ‘Zilliya’, bata kama kowa ba ranar Lahadi a karon farko tun Faburairun 2020

A karon farko tun bullowar Korona a kasar nan wato Fabrairu 2020, ba ta kama kowa ba a Najeriya ranar Lahadi.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta sanar da haka a shafinta dake yanar gizo ranar Litini da yamma.

Jinkirin samun bayanai game da cutar ya biyo bayan hana shafin tiwita aiki a Najeriya da gwamnatin Buhari ta yi.

Rashin samun wanda ya kamu da cutar

Rashin samun wadanda suka kamu da cutar ya zama babban nasara a yaki da korona da Najeriya ke yi.

Tun a watan Maris kasar nan ta fara samu raguwar yaduwar cutar a Najeriya.

A ranar Asabar adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar a rana ya ragu zuwa 51 sannan daga nan ba a samu ko daya ba ranar Lahadi.

Najeriya ta yi tsawon makonni 2 ba tare da ta samu wanda cutar ta kashe ba.

Duk da haka jami’an lafiya sun yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin Korona don gujewa kamuwa da cutar domin akwai yiwuwar wasu na dauke da cutar ba tare an san da zaman su ba saboda rashin yin gwajin cutar.

Zuwa yanzu mutum 167,206 suka kamu da cutar sannan mutum 2,117 sun mutu.

Mutum 1,532 na killace a asibiti, an yi wa mutum sama da miliyan 2 gwajin cutar a Kasar nan.


Source link

Related Articles

63 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button