Labarai

‘Yan sanda na farautar matashin da ya kashe Wansa da wuka

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa ta fara farautar wani matashi mai shekara 22 da ya kashe wansa da wuka a jihar.

Jami’in hulda da jami’a na rundunar Lawan Shiisu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Litini a garin Dutse.

Shiisu ya ce wannan abin tashin hankali ya auku ranar 5 ga Janairu a kauyen Sabuwa Takur dake karamar hukumar Dutse.

Ya ce rundunar ta samu labarin cewa matashin ya caka wa wansa wuka wan ya mutu a asibitin koyarwa na Rashid Shekoni dake Dutse yayin da likitoci ke duba shi.

Shiisu ya ce nan da nan sai rundunar ta nufi asibitin inda mahaifin yaran Julius Ochai mai shekara 65 ya bayyana cewa dansa Alfred Julius mai shekara 22, ya kashe wansa Augustine Julius mai shekara 30 da wuka bayan sun samu rashin jituwa a tsakanin su.

“Ochai ya ce Alfred ya gudu sannan Augustine ya rasu yayin da likitoci ke duba shi.

Shiisu ya ce tare da hadin gwiwar iyalin Ochai rundunar ta fara farautar Alfred domin yanke masa hukunci bisa laifin da ya aikata.


Source link

Related Articles

196 Comments

  1. Pingback: 1florists
  2. Pingback: faree gay chat
  3. Pingback: gay chat louisiana
  4. Pingback: hollywood slots
  5. Pingback: games slots
  6. Pingback: murka slots

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news