Labarai

YAYI AMAI YA LASHE: Fasto Mbaka ya janye sukar da ya yi wa Peter Obi, ya nemi afuwar sa

Idan ba a manta ba Babban Limamin Ɗariƙar Katoliƙa ɗin nan dake Jihar Anambra, Peter Maka, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ba zai taɓa zama shugaban ƙasa a 2023 ba.

Mbaka ya ce Obi, wanda ke takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP, tantirin marowaci ne, don haka da a ce mai jini a jika ke shugabancin, amma marowaci, har gara a ce wani dattijo ne ke mulki, amma kuma mai hannun kyauta.

Mbaka ya yi wannan kalami a cocin sa inda ya ke wa’azi wato, Adoration Ground, Enugu a ranar Laraba.

“Yanzu yunwa ta sa mutane gaba, kuma a wannan irin mawuyacin hali da ake fama za a kinkimo mana Peter Obi tantirin marowaci a ce ya zama shugaban ƙasa?

“Ta yaya mutumin da kuɗin sa ba su ɓamɓaruwa daga hannun sa zai zama shugaban ƙasa? Ku na son yunwa ta kashe ku ne? Jama’a shin ko dai kun kwarkwance ne?

“A yanzu na san Atiku Abubakar da gaske neman kujerar shugaban ƙasa, tunda bai tattago Peter Obi mataimakin takarar sa ba.

“Mu dama mutumin da ke yin abu da gaske mu ke nema. Idan Peter Obi bai zo nan ya durƙusa nan ya bada haƙuri ba, to idan ya zama shugaban ƙasa zan rufe wannan cocin. Ballantana ma ba cin zai yi ba. Ko ƙamshin kujerar ma ba ji zai yi ba.

Idan ba a manta ba, Mbaka ya ragargaji Obi a zaɓen 2019, lokacin da Obi ya ƙi bai wa cocin sa gudummawar kuɗi.

Sai dai kuma daga baya Mbaka ya bai wa Obi haƙuri, ɗaga baya kuma ya ce an matsa masa lamba ne ya ba shi haƙurin, ba da son ran sa ba.

“Na yi ne a matsayin nuna biyayya ta ga Bishof na Ɗariƙar Katoliƙa, wanda ya sa na ba shi haƙuri.

“Kai bari na faɗa maku gaskiya, idan ƙabilar Igbo na neman shugabanci, to ba irin su Peter Obi ya dace su yi takara ba.” Inji Mbaka.

“Na kira Atiku a lokacin kamfen ɗin 2019, na ce masa za ka zama shugaban ƙasa, amma sai fa idan ka yi watsi da Peter Obi. Saboda shi akwai tsinuwar Ubangiji rataye awuyan sa. Idan ka na son zama shugaban ƙasa, to ka canja shi.”

Mbaka ya ce bai yi nufin tozarta shi da kalaman da yayi ba.

A karshe ya yi masa fatan Allah ya bashi sa’a a takarar da yake yi na zama shugaban kasa.


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. สล็อต pg ทดลองเล่น ใน pantip เล่นเกมเเล้วได้ความสนุกสนานต้องเกม pg slot ทดลองเล่นได้ไม่มีพันทิปก็เล่นได้ เเค่คลิกไปที่เว็บไซต์ของของเราแล้วเล่นได้เลย คุณจะได้รับความสนุกกับแสงสีเสียงที่คมชัดแบบสุดๆ ภาพการ์ตูนน่ารักๆอย่างแน่นอน

  2. ทางเข้าเล่น pg slotเว็บสล็อต ที่คนนิยมเล่นเยอะที่สุด ต้องยกให้เว็บ พีจีสล็อต ยืน 1 เว็บตรงสล็อตpg วันนี้เราอัปเดตเว็บใหม่ ใช้ระบบทันสมัย ที่สุด ฝากถอน รวดเร็ว

  3. Hello, Neat post. There’s an issue with your website in internet explorer, might check this… IE still is the marketplace chief and a large component to people will omit your great writing because of this problem.

  4. Great V I should certainly pronounce, impressed with your site. I had no trouble navigating through all the tabs as well as related information ended up being truly simple to do to access. I recently found what I hoped for before you know it at all. Quite unusual. Is likely to appreciate it for those who add forums or anything, site theme . a tones way for your client to communicate. Nice task..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button