Labarai

ZAƁEN FIDDA GWANI: Fintirin Adamawa, Kashim ɗin Bauchi, Uban Makurɗi, Abachan Kano, Ashirun Kaduna sun yi nasara zaɓe na Jam’iyyar PDP

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a Yola babbabn birnin jihar Adamawa.

Shugaban Kwamitin zabe na jihar Gibon Katabs ya bayyana cewa Fintiri ne kadai ya yi takarar kuma ya samu ƙuuri’u ya samu ruwan kuri’u 663 cikin 668 da aka jefa, an samu lalatattu ƙuri’u 5.

Haka kuma a jihar Bauchi, ɗan takara ɗaya tilo da ya fito takarar kujerar gwamnan jihar Ibrahim Kashim ne aka zaba ɗan takarar gwamnan jihar.

Kashin ya zama dan takaran gwamna na jami’yya PDP.

Shugaban kwamitin zaben wanda kuma shine ya sanar da sakamakon zaɓen Hassan Grema ya ce Kashim ya samu ƙuri’un deliget 655.

A jihar Benuwai, Titus Uba ne ya lashe zaɓen fidda gwani na ƴan takarar gwamnan jihar na PDP.

Jihar Kano kuwa, wakilai sun zaɓi ɗan tsohon shugaban kasa Mohammed Abacha ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.

Malamar zabe na jihar Amina Garba ta ce a zaben da aka yi ranar Laraba Abacha ya samu kuri’u 736 shi kuma abkin takarar sa Jafar Sani-Bello ya samu kuri’u 710.

A jihar Barno kuma Mohammed Jajari ya lashe zaɓen .
Jihar Jigawa kuwa, ɗan tsohon gwamnan jihar ne, Mustapha Sule Lamido ya yi nasara a zaben gwamnan.

Sai kuma Kaduna garin gwamna in da Isah Ashiru ya lallasa ƴan takara 4 a zaɓen fidda gwanin. Isah ya kada fitattun ƴan siyasan jihar da suka fafata da shi a takarar.

A jawabin da Isah Yayi bayan nasara da ya samu, ya yi kira ga sauran ƴan takaran da su zo a haɗa hannu gaba ɗaya domin samun nasarar jam’iyyar.


Source link

Related Articles

3 Comments

  1. Howdy! I simply wish to give you a huge thumbs up for the
    excellent information you have right here on this post.
    I will be returning to your blog for more soon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news