Ciwon Lafiya

Za a fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar a kasar Birtaniya

Ma’aikatan kiwon lafiya na kasar Birtaniya bisa umarnin gwamnatin kasar za ta fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona da maganin AstraZeneca/Oxford a wasu asibitocin dake kasar.

Gwamnatin ta ce asibitoci biyu dake garin Landan, daya a Kudancin Ingila, daya a Arewacin Ingila, daya a Midlands da daya a Oxford sune asibitocin da za su fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar daga ranar Litini.

Za a rika yi wa mutane rigakafin a rumfunar yin rigakafin sama da 700 da aka kakkafa a wadannan wurare sannan tsoffi da sabbin ma’aikatan hukumar lafiya NHS dake Ingila da wasu da suka kammala samun horo a yanar gizo ne jami’an lafiyan da za su rika yi wa mutane rigakafin.

Gwamnati ta kuma ce za ta biya likita da nas-nas karin dala 13 a dalilin yi wa mutane allurar rigakafin a gida daga nan har zuwa karshen wata.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda masana ilmin hada magunguna dake aikin hada maganin rigakafin cutar Korona sun ce nan da karshen 2021 kowa da kowa zai samu maganin rigakafin cutar Korona.

Malaman dake aiki da kamfanin BioNTech da Oxford ne suka fadi haka a taron tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar da UN ta shirya.

Zuwa yanzu kasar UK ita ce ƙasa ta farko a duniya da ta amince da maganin rigakafin korona da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka hada.

Gwajin sahihanci da ingancin maganin da hukumar MHRA ta yi ya kai kashi 95.

Tuni wadannan kamfanonin sun fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar da maganin da suka hada a Disamba.


Source link

Related Articles

175 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button