Labarai

Za mu ceto Zamfara daga tsananin hare-haren Ƴan bindiga

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya jaddadawa Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal cewa zai yi aiki tuƙuru wurin ganin jam’iyyar PDP ta lashe zaɓen 2023 a Jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana haka ne jiya Laraba a gidan sa da ke Abuja, yayin da Dauda Lawal ya jagoranci tawagar ‘ya’yan PDP na Jihar Zamfara tare da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da suka sauka sheƙa daga APC zuwa PDP.

Atiku ya ce, hanya daya ce za a iya bi wurin ceto Zamfara, shi ne ta hanyar korar APC daga mulki.
“Ba za mu samar da nagartacciyar rayuwa ga jama’a ba har sai mun tabbata mun kori APC, wanda kuma hakan na buƙatan hadin kai.

“Babban abin da mutanen Zamfara ke buƙata a yanzu shi ne zaman lafiya. A samar da tsaro a gonaki, a samar da ayyukan yi. Idan aka yi haka, za a samu inganci a komi na rayuwa” Inji shi

Tun farko a jawabinsa, dan takarar gwamna na PDP a Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana dalilin wannan ziyara a matsayin gaisuwa tare da gabatar da jiga-jigan ‘yan siyasar da suka sauya sheƙa daga APC zuwa PDP. Haka nan kuma don taya murna ga Atiku bisa nasarar da ya samu a zaben fidda gwanin PDP wanda aka yi kwanakin baya.

Lawal ya ce, ‘yan Nijeriya sun gaji da APC, a shirye suke da su zabi PDP a matakin jihohi da ma tarayya. “Samun waɗannan manyan ‘yan siyasa su sauya sheka daga APC zuwa garemu, ba ƙaramar nasara ba ce ga PDP”. Inji shi.

Daga cikin jiga-jigan da suka sauya shekan daga APC zuwa PDP akwai Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi, Alhaji Sahabi Liman Kaura, Alhaji Illili Bakura, Engr. Garba Ahmad Yandi, Hon. Iƙra Bilbis, Dr. Na’Allah Isa Mayana, Hon. Mukhtar Lugga da sauransu.

Kafin kammala ziyarar, Dauda Lawal ya gabatarwa da Atiku da kyautar rigar saka a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da Zamfara ta shahara da su a baya.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. My wife and i felt excited Louis could round up his research through your ideas he had from your own weblog. It’s not at all simplistic just to continually be freely giving things people today may have been selling. And we realize we have got the website owner to give thanks to because of that. Those explanations you have made, the straightforward site navigation, the friendships you give support to create – it is mostly extraordinary, and it is helping our son and us consider that that article is fun, and that is rather important. Thank you for the whole lot!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button