Labarai

Zailani ya yi wa ƴan APCn Igabi ruwan kuɗi a Kaduna

Kakakin majalisar Kaduna Yusuf Zailani ya yi wa mutanen mazaɓarsa ambaliyar dubban nairori.

Zailani ya raba wa ƴan APC 6000 naira 10,000 kowannen su kyata kowa ya je ya sha ruwa sakamakon kokari da kuma hidima da suka rika yi wa jam’iyyar APC a rumfuna da gundumomin su.

Wadanda suka amfana da wannan kyauta sun fito daga nazabu 600 da ke ƙarkashin karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Ɗan takarar Sanata na Kaduna ta tsakiya Mohammaed Sani Dattijo, ya halarci taron rabon kuɗin.

Dattijo ya yabawa Zailani bisa wannan kokari da ya yi wa mutanen mazabar yankin ƙaramar hukumar Igabi.

Waɗanda aka zaɓa gaba ɗayan su kaf sun yi layi ne ana farke ɗaurin naira dubu-dubu ana ƙirga goma sai a ɗanka maka.

Wadanda suka amfana da wannan kyata sun gode wa ɗan majalisar sannan sun yi alwashin ganin APC ta yi nasara a zaɓe mai zuwa.

Sai dai kuma wad’su daga cikin ƴan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar sun bayyana cewa hakan ba zai hana jam’iyyar shan kashi a zaɓe mai zuwa ba a jihar.

” Kan mage ya waye, mutane za su hisu su karɓi kudin, dama dai kuɗin su ne, ku karba amma ku zaɓe abinda ya dace. ” In ji wani ɗan PDP a Kaduna.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *