Labarai

Zan fi maida hankali wajen bunkasa Ilimi a Kasar nan

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana wa dandazon magoya bayan sa da jam’iyyar NNPP a jihar Legas cewa idan ya zama shugaban Kasa, zai fi maida hankali ne wajen bunkasa ilimi a kasar nan.

Kwankwaso ya bude ofishin kamfen dinsa a unguwar Ikorodu dake birnin Ikko.

Dubban mutane ne suka halarci taron bude ofishin har da wasu daruruwa da suka canja sheka daga wasu jam’iyyun zuwa jam’iyyar NNPP a Legas.

Bayan haka ya ce matasa ne za su zamo kan gaba a cikin gwamnatin sa.

Jihar Legas dai ita ce cibiyar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.

Sauran ‘yan takarar da Kwankwaso zai fafat da su sun hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na LP, da wasu yan takara na jam’iyyun kasar nan.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. I’ve been searching for hours on this topic and finally found your post. totosite, I have read your post and I am very impressed. We prefer your opinion and will visit this site frequently to refer to your opinion. When would you like to visit my site?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button