Labarai

ZARGIN HAƊA BAKI DA ‘YAN TA’ADDA: Hukumar SSS ta janye tuhumar da ta ke wa Tukur Mamu

Hukumar Tsaro ta SSS ta janye tuhuma da zargin ta’addancin da ta yi wa Tukur Manu, mai shiga tsakanin ‘yan ta’addar da su ka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a ƙarshen Maris.

Bayan sun kama Mamu, SSS sun ce sun samu kakin sojoji da wasu kuɗaɗe a gidan sa.

An kama shi cikin Satumba, bayan ya yi ta shiga tsakani ‘yan ta’adda na sakin wasu da su ka tsare rukuni bayan rukuni.

An tsare shi ne a Masar, a ranar 6 Ga Satumba, aka dawo da shi Najeriya.

SSS sun nemi kotu ta ba su ikon tsare shi har tsawon kwanaki 60 domin su ci gaba da binciken sa.

A ranar Alhamis ɗin nan ce kotu ta sa ranar fara sauraren gabatar da Mamu a kotu.

Sai dai kuma yayin da aka je Kotun Tarayya a ranar Alhamis ɗin, lauyan SSS mai suna A.M Ɗanlami, ya shaida wa Mai Shari’a Nkeonye Maha cewa SSS sun amince da janye tuhumar da su ke yi masa.

Ɗanlami ya ce dangane da batun Tukur Mamu, yanzu dai sawun giwa ya take na raƙumi. Don haka sun janye tuhumar da su ke yi masa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button