Labarai

ZARGIN RASHIN ADALCI A TAKARAR SHUGABAN ƘASA: Kalu ya janye shiga takara, ya goyi bayan takarar Sanata Ahmad Lawan

Bulaliyar Majalisar Dattawa, kuma Sanata mai wakiltar Abiya ta Arewa, Orji Kalu, ya bayyana janyewar sa daga takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Kalu ya sake nanata cewa ya janye ne saboda yadda ake ta samun tururuwar ‘yan takara daga kudu, maimakon su yi adalci su bar wa ƙabilar Igbo kaɗai su fitar da wanda zai yi shugaban ƙasa daga cikin su.

Dama a baya Kalu ya ce zai tsaya takara ne kaɗai idan jam’iyyar APC da PDP sun bai wa yankin da ya fito, wato Kudu maso Gabas damar shugabancin Najeriya a 2023.

A makon jiya ne ya bayyana barazanar janyewar sa, tare da ragargazar dukkan wani ɗan takara na APC da PDP wanda ya fito daga yankin Neja Delta da yankin Kudu maso Yamma na Yarabawa.

Kalu ya ce sun yi wa yankin ƙabilar Igbo rashin adalci, domin su ya kamata a bai wa damar mulkin Najeriya a 2023.

Na Koma Goyon Bayan Takarar Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa -Kalu:

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Kalu ya ce “a yanzu ina goyon bayan takarar Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, wanda shi ma ya cancanta, saboda yankin su na Arewa maso Gabas bai taɓa yin shugabancin Najeriya ba.”

Ya ce ya so a ce yankin Kudu maso Gabas ne ya yi mulki a 2023, amma tunda ‘yan zalama sun yi kane-kane, a yanzu ya janye, amma ya na goyon bayan Ahmad Lawan.

A ƙarshe ya ce ya sayi fam na sake tsayawa takarar Sanatan Abiya ta Arewa, “domin na ci gaba da ayyukan alherin da na sa a gaba wajen samarwa a yankin mazaɓa ta.” Inji Kalu.

‘Yan Takara Daga Kudu Ba Su Yi Wa Ƙabilar Igbo Mutunci Ba -Kalu:

Orji Kalu ya yi tir da ‘yan takara daga Kudu-maso-yamma da na Kudu-maso-kudu, ya ce zai janye tunda ba su ganin mutuncin ƙabilar Igbo.

Bulalar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu wanda ke neman fitowa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya yi tir da duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya fito daga Kudu-maso-yamma da na Kudu-maso-kudu.

Ya ce tunda ba su ganin daraja da mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, ballantana har su yi adalci su bar wa yankin takarar shugaban ƙasa, to shi zai janye daga shiga takarar.

Haka Kalu ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Kalu bai ware ɗan takarar APC ko PDP ba, ya ce kamata ya yi su mutunta haƙƙin zamantakewa duk su janye su bar wa ɗan ƙabilar Igbo ya fito takarar shugabancin ƙasar nan.

Idan ba a manta ba, a farkon wannan watan ne Kalu ya ce zai fito takara a ƙarƙashin APC, idan har aka bar wa ‘yan ƙabilar Igbo su yi shugabancin Najeriya cikin 2023.

Ya zargi ‘yan takarar da su ka fito daga kudu da yi wa ƙabilar Igbo rashin adalci.

Kalu ya daɗe ya na kakabin neman a yi adalci a bar ‘yan ƙabilar Igbo su yi takarar shugabancin ƙasa a 2023 a tsakanin su.

Kalu ya ce duk da ya na son tsayawa takarar shugabancin Najeriya, to ba zai iya ƙaddamar da takarar sa, ba tare da goyon bayan yankin Kudu-maso-kudu da Kudu-maso-yamma ba.

Saboda haka ne ya ce ba shi da zaɓi, sai dai ya “koma Majalisar Dattawa, ya nesanta kan sa daga zaɓen shugaban ƙasa ko takarar zaɓen.”

“Ina mamakin ganin yadda ‘yan takara suka fito birjik daga Kudu-maso-yamma da Kudu-maso-kudu daga ɓangare biyu, wato APC da PDP. Abin kunya ne sosai, ganin yadda ba su ko ganin kima ko mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, wanda bai taɓa samar da shugaban ƙasa mai cikakken ikon dimokraɗiyya ba.

“Na yi tunanin za su tuna da mu su goya mana baya, ɗan Kudu-maso-gabas ya yi shugabanci a 2023. Amma idanun su sun rufe, sai bindiga suke ta yi da kuɗi. Sun manta kuɗi ba ya sayen kujerar shugaban ƙasa.”


Source link

Related Articles

4 Comments

 1. Its like you read my mind! You seem to know so much about this, like you
  wrote the book in it or something. I think that you can do with some pics
  to drive the message home a bit, but instead of that,
  this is great blog. A fantastic read. I’ll certainly be back.

  Check out my web site; Bookmarks

 2. Greetings! This is my 1st comment here so I just wanted to give a quick shout out and say I
  genuinely enjoy reading through your posts. Can you suggest any other blogs/websites/forums that go over the same topics?
  Thanks for your time!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news