Labarai

ZARGIN TUGGU DA MAƘARƘASHIYA A PDP: Da na ga dama da na hargitsa zaɓen fidda-gwani, kowa ya rasa -Gwamna Wike

Gwamna Nyesom Wike ya zargi Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da wani Gwamnan Kudu maso Kudu da cin amanar sa da kuma shirya masa maƙarƙashiya a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa, wanda aka yi a ranar Asabar a Abuja.

Wike ya yi wannan kakkausan kalamai ne a Fatakwal, wurin gangamin da aka shirya domin tarbar sa, bayan ya koma gida daga wurin zaɓen fidda-gwanin da ya samu ƙuri’u 237. Atiku Abubakar ne ya kayar da shi, bayan ya samu ƙuri’u 371. Bukola Saraki ya samu ƙuri’u 70, yayin da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom ya samu ƙuri’u 31.

Wike ya yi zafafan kalamai ne sakamakon maƙarƙashiyar da ya ce an shirya masa a wurin taron, yadda shugabannin jam’iyyar PDP su ka bari Tambuwal ya janye daga takara, alhali a lokacin bai kamata ya janye ba, saboda lokacin janyewar ta sa ya wuce.

A bayanin Wike, ya ce Kwamitin Tantance ‘Yan Takara a zalunce shi, domin ya bayar da dama ga Tambuwal ya yi magana sau biyu. Hakan kuma a cewar Wike, an karya ƙa’idar zaɓen fidda-gwani.

“Da na so tayar da fitina, da sai na tashi daga inda na ke na je na ce ban yarda a ci gaba da taron ba. Saboda an bai wa Tambuwal lokacin da ya zarce na kowa, kuma na ƙa’ida, har ya yi dogon jawabin cewa ya janye, ya goyi bayan Atiku Abubakar.

“Amma saboda ba na son tayar da fitinar da za ta hargitsa PDP baki ɗaya, sai na haƙura don a zauna lafiya.

Wike dai ya yi raga-raga da shugabannin PDP, ya ce kwata-kwata babu adalci a lamarin su.

Da ya koma kan Gwamnonin Kudu maso Kudu, Wike ya ce wanda ya ci amanar sa bai rage shi da komai ba, amanar kan sa ya ci.

Bisa alama ya na magana ne kan Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, wanda wakilan zaɓen ‘yan takarar jihar sa su ka zaɓi Atiku, maimakon Wike, kamar yadda shi Okowa ɗin ya sha cewa ɗan Kudu za su zaɓa.

“Na taya Atiku murna don a tafi tare, kuma jam’iyya ta kauce wa ruɗani. Na sanar da shi da ya zo gida na a Abuja cewa na ga wasu tarkacen gwamnoni da ‘yan miya-ta-yi-zaƙi na bin ka ɗuuu. To waɗannan duk fanko ne, ba su da mutane. Ni ke da mutane, kuma ta tabbatar zaɓe ya nuna haƙa.”

Masu nazarin siyasa na ganin cewa magoya bayan Tambuwal da na Gwamnan Delta ne su ka ƙara wa Atiku yawan ƙuri’u, har ya kayar da Wike.”

Gwamna Wike ya ce tunda Kudu ba su da haɗin kai, daga yau kada wani maras kunya ya fito ya ce Arewa ta danne su, domin su ne su ka danne kan su.

Idan ba a manta ba, Wike ya goyi bayan Tambuwal a zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP.


Source link

Related Articles

15 Comments

  1. Attractive component to content. I simply
    stumbled upon your blog and in accession capital to assert that I get in fact loved account your blog posts.
    Anyway I’ll be subscribing for your augment and even I fulfillment you get
    admission to constantly rapidly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button